Studies in African Languages and Cultures (Dec 2006)
The syntactic functions of weak verbal nouns in Hausa
Abstract
Wannan maƙala ta gabatar da tunanin rarraba sunaye ’yan aikatau. Masanan harshen Hausa suna kiransu sunaye ’yan aikatau masu dafa-ƙeya -'wâ. Na nuna cewa ma’anarsu ta ƙamus ba ta dace da ma’anar ta ƙirar jimla ba. Ko da yake sigarsu ɗaya ce, wato duk daga cikinsu suna da ɗafa-ƙeya -'wâ, irin wannan siga ba kullum take ɗauke da ma’ana ɗaya kawai ba. Ana yin amfani da su wajen ginin harshe dabam-dabam. Suna yin aikin sunaye ko mubtada ko ganga. Akwai abubuwa guda biyu waɗanda suke fahimtar aikinsu da ma’anarsu — tsarin jumloli nasu da kuma kalmomin da suka kewaya su, wato kalmomi da suka mulki kamar zaruffa, ɓangaren mallaka, siffofi da mafayyata